23 Agusta 2025 - 15:53
Source: ABNA24
Hadin Kai Na Gaskiya Ne Kawai Zai Iya Dakatar Sahayoni/Sabani Ba Abunda Zai Haifar Sai Koma Baya Da Rushewar Al'ummah.

A wajen taron "Hadin kai na Musulunci da batun Palastinu", masu jawabai sun jaddada cewa, matukar ba’a samar da hadin tsakanin kasashen musulmi ba, gwamnatin Sahayoniya ba za ta kawo karshen laifukan ta’addanci a Gaza da wahalar da al'ummar Palastinu suke sha ba.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya kawo cewa: a daidai lokacin da ake ci gaba da tsanantuwar laifuffukan gwamnatin sahyoniyawan a zirin Gaza, da kuma ci gaba da yin shirun hukumomin kasa da kasa, musamman ma wasu daga cikin sarakunan larabawa da na Musulunci, da manyan malamai da manazarta harkokin siyasa na ganin cewa hanya daya tilo da za a kawo karshen wahalhalu da bakin ciki da al'ummar Palastinu suke ciki ita ce hada kan al'ummar musulmin duniya tare da neman 'yancin kai na duniya. An kuma jaddada wannan batu a taron "Haɗin kan Duniyar Musulunci da Batun Falasɗinawa".

Taron wanda ya gudana a kamfanin dillancin labarai na ABNA tare da halartar manyan malamai uku daga jami'o'in kasar Turkiyya, Farfesa Dr. Hamdi Gundogar, shugaban tsangayar ilimin tauhidi na jami'ar Adiyaman, Dr. Selim Guverdi, malami a tsangayar ilimin tauhidi na jami'ar Istanbul, da Farfesa Dr. Rahmat Yildiz, babban malami a jami'ar Ataturk, sun bayyana ra'ayinsu kan wajabcin hadin kan musulmi.

Duk Da Yawan Al'umma Biliyan Biyu, Har Yanzu Musulmi A Kansu A Watse Ya Ke!

A yayin da yake ishara da irin gagarumin karfin da duniyar musulmi take da shi, Farfesa Hamdi Gundogar a cikin jawabin nasa ya ce: A yau, fiye da musulmi biliyan biyu ne ke rayuwa a duniya, kuma galibin albarkatun makamashi da yawan matasa da kuma matsayi na siyasa suna hannun kasashen musulmi; amma wannan yuwuwar ta kasance ba ta da tasiri saboda rashin haɗin kai. Yayin da Turai, duk da bambancin addini da siyasa, ta kafa Tarayyar Turai, kuma ana mulkin Amurka daga cibiya mai jihohi 50, Amma Musulmi sun fada cikin ƙananan bambance-bambance, wanda ya raunana su.

Yayin da yake ishara da rikicin Gaza, shugaban tsangayar ilimin tauhidi na jami'ar Adiyaman da ke kasar Turkiyya ya jaddada cewa: Idan kasashen musulmi suka hade kansu, da Isra'ila ba za ta taba kuskura ta haddasa irin wannan bala'i ba. A yau sama da mutane 60,000 da ba su ji ba ba su gani ba ne suka yi shahada a Gaza, kuma hakan ya faru ne kawai sakamakon rarrabuwar kawuna a kasashen musulmi. Batun Falasdinawa ba batu ne na Palasdinawa kadai ba, a’a lamari ne da ya shafi dukkanin musulmi.

Komawa Ga Alqur'ani Da Sunna Shine Mabudin Hadin Kai

وَالَّذِينَ كَفَرُوا بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ إِلَّا تَفْعَلُوهُ تَكُنْ فِتْنَةٌ فِي الْأَرْضِ وَفَسَادٌ كَبِيرٌ (73)

Bugu da kari, Dr. Selim Gulverdi ya tunatar da cewa wajibi ne a yi bitar mahangar al'ummar musulmi dangane da abubuwan da suka faru a baya inda ya ce: Domin hadin kai muna bukatar tushe mai karfi, kuma wannan tushe ba komai ba ne face Alkur'ani mai girma da Sunnar Annabi Muhammad (SAW) ingantacciya. Abin takaici, mun sha sake farfado da bambance-bambancen tarihi da na siyasa na baya kuma mun mayar da shi wani lamari na imani. Wannan dabi'a ba ta da wata anfani face koma baya da raunanan Al’umma.

Wannnan malami a tsangayar ilimin tauhidi na jami'ar Istanbul ya kara da cewa: Wariyar launin fata da kabilanci su ma manyan abubuwan da ke kawo cikas ga hadin kai. Kasancewa Baturke, Balarabe, Kurdawa ko Farisa ba gata ba ne, sai dai nufin Allah ne. Ya kamata a kalli waɗannan bambance-bambance a matsayin kadarorin al'adu da bambancin, ba kayan aikin kunna gaba ba. A yau, fiye da kowane lokaci, ya kamata mu bayyana kanmu kawai da ainihin mu na Musulunci.

Farfesan jami'ar ya jaddada cewa kulla alaka kai tsaye tsakanin al'ummar musulmi na iya rage rashin fahimtar juna sannan ya kara da cewa: A Turai, mutane na tafiya ba tare da ketare iyaka ba. Me ya sa mu musulmi ba mu da irin wadannan wurare na zirga-zirgar 'yanci? Kusancin al'ummomi zai haifar da kyakkyawar fahimta da kawar da ra'ayi mara kyau.

Ana Samun Hadin Kai Ta Hanyar Aiki, Ba Wai Yin Taken Ba

Mai magana da yawun zaman na uku, Farfesa Rahmat Yildiz, shi ma ya jaddada wajibcin daukar matakai na zahiri kan hanyar hadin kai tare da cewa: Ba a samun hadin kai kawai ta hanyar magana da maganganu ba. Cibiyoyi irin su kungiyar hadin kan Musulunci wajibi ne su kara kaimi, da yunkuri na gaske, kuma su kasance masu karfin matsin lamba kan makiya al'umma. Har ila yau, wajibi ne kasashen musulmi su samar da hadin gwiwa na hakika a fannonin tattalin arziki, kasuwanci, tsaro da kuma kafofin watsa labarai. Idan Turai ta sami damar gina irin wannan ƙawance, me ya sa ba za mu iya ba?

وَالَّذِينَ كَفَرُوا بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ إِلَّا تَفْعَلُوهُ تَكُنْ فِتْنَةٌ فِي الْأَرْضِ وَفَسَادٌ كَبِيرٌ (73)

Haka nan kuma ya yi suka kan matsayin da kasashen musulmi suka dauka kan laifukan gwamnatin sahyoniyawan ya kuma bayyana cewa: Da a ce kasashen musulmi sun yanke alakarsu da Isra'ila tare da kakaba mata takunkumin tattalin arziki mai tsanani, da ba mu ga irin wannan kisa a zirin Gaza a yau ba. Hadin kan gaske kawai zai iya dakatar da injin yaƙin Sahyoniyawa.

A karshen taron, malaman jami'o'in kasar Turkiyya sun mika godiyarsu ga kamfanin dillancin labarai na ABNA da gudanar da wannan taro da makamantansu, inda suka jaddada irin rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen bayyana gaskiya da kuma karfafa hadin kan manyan kasashen musulmi.

Da suke bayyana cewa ya kamata kafafen yada labarai su zama harshen al’umma, wadannan farfesoshi sun kara da cewa: Kafofin yada labarai masu gaskiya za su iya kawar da rashin fahimtar juna da zama wata gada tsakanin kasashe. Ƙarfafa kafofin watsa labaru na Musulunci yana da mahimmanci kamar hadin kan siyasa da tattalin arzikin ƙasashen musulmi.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha